✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tono gawar basarake Onisa na Ilora bayan watanni 17 da binne ta

An kawo karshen takaddama a kan batun tono gawar basarake Onisa na Ilora Cif Lawrence Owoade, wanda ake zargin ya rataye kansa watanni 17 da…

An kawo karshen takaddama a kan batun tono gawar basarake Onisa na Ilora Cif Lawrence Owoade, wanda ake zargin ya rataye kansa watanni 17 da wucewa da aka yi masa jana’iza da binne shi ba tare da yin binciken gano dalilin mutuwarsa ba.
Kafin a yi masa jana’iza a matsayin mutumin da ya kashe kansa a wancan lokaci sai da aka gayyato dodanni da suka yi wa gawar tsubbu da suka binne ta ba tare da sanin danginsa ba. Jami’an ’yan sanda daga shiyya ta 11 da ke Osogbo da hadin gwiwar wakilai daga ma’aikatun kiwon lafiya da tsaftace muhalli na Jihar Oyo da wani likitan bincike daga Asibitin Koyarwa na UCH da ke Ibadan, su ne suka gudanar da aikin tono gawar mamacin domin yin binciken musabbabin mutuwarsa da mika gawar ga danginsa domin sake yi masa jana’izar karramawa da sake binne shi a wani wuri daban.
An tono gawar ce a gaban dan uwan marigayin Cif Olayiwola Owoade, wanda ya jagoranci sauran dangi. Sai dai akwai wasu manyan mutane biyu masu suna Cif Sunday Aserifa da Cif Amidu Adeleke da ba su halarci wajen tono gawar ba, domin tun farko sun nuna rashin amincewarsu da yin hakan.
Rashin halartar wadannan manyan mutane duk da gayyatar da aka yi masu kafin isowar wannan rana bai hana ci gaba da gudanar da wannan aiki da Mataimakiyar Sufeto Janar shiyya ta 11 da ke Osogbo, Uwargida Kalafite Adeyemi ta bayar da umarnin gudanarwa ba. An shafe awoyi 3 ana gudanar da aikin tono gawar cikin tsauraran matakan tsaro a karkashin jagorancin ASP Bolaji Alao na rundunar SARS da ke wannan shiyya.
A lokacin da aka tono kabarin marigayin da ke cikin gonarsa a garin Ilora, an samu kokon kawuna guda 2 da suka yi kama da na akuya da wata karamar tukunya da kayan tsafi a cikinta da aka girke su kusa da kasusuwan gawar a cikin makarar da aka binne su tare. An yi zargin cewa, Cif Lawrence Owoade, a matsayinsa na mutum na 2 daga Sarki wato, (magajin gari) shi ne ya rataye kansa a cikin gonarsa a ranar 20 ga watan Nuwamba, shekara ta 2014 kuma aka binne shi da umarnin Sarkin Ilora ba tare da binciken musabbabin mutuwarsa ba.
Wani abokin marigayin mai suna Elder Francis Afolabi Morakinyo, shi ne ya aika da rubutacciyar takardar kara zuwa ga Sufeto Janar na ’yan sanda Mista Solomon Arase, da ya nemi a yi binciken kwakwaf domin gano ainihin abun da ya yi sanadin mutuwar abokin nasa. Cif Morakinyo wanda yayi zargin cewa kisan gilla aka yi wa amininsa, ya ce bai ga dalilin da zai sa Cif Owoade ya rataye kansa ba, domin babban mutum ne da ke rike da mukami na 2 daga sarki kuma manomi ne da ya mallaki babbar gonar kiwon kaji da wasu manyan filaye da kadarori a Ibadan da Ilora.