Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da Gwamnan Mutfwang ya yi a ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana hare-haren a matsayin ayyukan ta’addanci da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye haƙƙinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu.
Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare.
Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci, inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.
Ya ce “ina jinjina wa masu ba da agajin gaggawa da jami’an tsaro bisa gagarumin matakin da suka ɗauka.
“Ina kuma gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci cikin gaggawa.”
Muftwang ya ce dole ne al’ummomi su ba da himma wajen kare kansu a cikin iyakokin da doka ta tanada.
Ya ce “ina kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su sake farfaɗo da sintiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.
“Dole ne mu haɗa kai don kare ƙasarmu, domin tabbatar adalci yayin da mu ke la’akari da kiyaye dokokin ƙasa.”
Aƙalla mutane 51 ne rahotanni suka ce an kashe bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Miango a Ƙaramar Hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.
Harin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kashe mazauna fiye da 40 a wasu ƙauyuka biyar a ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu.
Hukumomin ƙasar dai na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun daƙile hare-hare a jihar da aka daɗe ana fama da rikicin ƙabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.