✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tashi baram-baram a taron Shugabannin ECOWAS da Buhari ya halarta a Ghana

Buhari ya ce duk wani matakin ladabtarwar da za’a dauka a tabbatar da cewar ba zai yi wa jama’ar kasar illa ba.

Shugabannin Kungiyar Bunkasa Tattalin Azrikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS sun tashi baram-baram a taron da suka gudanar ranar Asabar a Accra, babban birnin Kasar Ghana.

Shugabannin sun gaza cimma matsaya a tsakaninsu kan matakin da ya dace su dauka domin ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

A taron da suka gudanar domin karbar rahotanni daga kwamitocin da suka kafa da kuma shawarwari, shugabannin sun yanke hukuncin dage taron nasu zuwa watan Yuli mai zuwa domin ba da damar ci gaba da tuntuba.

Wata majiya daga wurin taron ta ce bayan tafka mahawara, shugabannin sun kasa cimma matsaya akan matakin da ya dace a dauka akan kasar Mali, wadda taki gabatar da shirin mika mulki ga fararen hula da kuma katse hulda da kungiyar G5 Sahel dake yaki da ’yan ta’adda.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da matsayin kasarsa a wajen taron cewar, duk wani matakin ladabtarwar da za’a dauka akan sojojin a tabbatar da cewar ba zai yiwa jama’ar kasar illa ba.

Tuni kungiyar ECOWAS da AU suka sanar da dakatar da wadannan kasashe daga cikin su da kuma bukatar gabatar musu da shirin da sojojin ke da shi na mayar da mulki ga fararen hula.