Garin Pataskum, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a Jihar Yobe bayan babban birnin jihar na Damaturu, ya cika ya batse da ’yan siyasa da masu kudi don ba da tallafin ginin masallacin Juma’ar garin.
Bikin kaddamar da asusun gina masallacin wanda ke hankoron tara Naira miliyan 550 ya sami halartar masu hannu da shuni daga sassa daban-daban na jihar.
- An harbe mutum 8 ’yan gida daya a masallaci a Afghanistan
- Cutar Murar Tsuntsaye: Manoman Kano sun tafka asarar N600m a watanni 2
Kimanin Naira miliyan 315 ne dai aka tara a lokacin daga cikin adadin, ko da yake har yanzu asusun taimakon a bude yake.
Yayin bikin, Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Riko na Jam’iyyar APC mai mulki, Mai Mala Buni ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda abin da ya kira jajircewar gwamnatinsa wajen yaki da ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Bayanin hakan dai kunshe ne a wata sanarwa da Babban Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan, Mamman Muhammad, ya raba wa da manema labarai a Damaturu ranar Lahadi.
Ya ce a shekara hudun da suka wuce, duk ’yan yankin ba su taba mafarkin tara jama’a irin haka ba saboda yanayin rashin tsaro.
Daga nan sai ya jinjina wa al’ummar jihar bisa kokarinsu, inda ya ce masu kai hare-haren Boko Haram sun kusa zama tarihi nan ba da jimawa ba.
Gwamnan ya hori al’umma da su ci gaba da jajircewa wajen yin addu’o’in neman yardar Allah da kuma magance matsalar kalubalen tsaron da ta addabi Najeriya.