A jiya Laraba an dauki Mamman Daura cikin wani karamin jirgi zuwa kasar Ingila domin nema masa magani.
Sai dai wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta karyata rahotonnin da ke cewa an kai shi Ingila ne saboda sarkewar numfashi da yake fama da ita. Majiyar ta ce tafiyarsa, ba ta da bambanci da wadda ya saba yi kafin bullar annobar COVID-19 ba.
“Ba tafiyar gaggawa ba ce, ya saba yi kuma ya dade yana son ya yi domin ganin likitansa amma bai yiwu ba saboda hana zirga-zirga da aka yi”, inji shi.
— Kusancinsa da Shugaba Buhari
Ana ganin tafiyar ba ta saba da wadda kawunsa Shugaba Buhari yake yi zuwa Ingilar ba.
Da yawa daga cikin mutane sun dauki Mamman Daura a matsayin wanda ya fi kowa kusanci da Shugaba Buhari a harkar mulkin kasa.
Kwanakin baya, Daura ya yi hirar da sashen Hausa na BBC inda ya bayyana ra’ayin cewar a bi cancanta wajen zabar shugabanni ba mulkin karba-karba ba.
Hirar tasa ta jawo cece-kuce da manyan jam’iyyun PDP da APC suka soki ra’ayin nasa inda kowacce ta sha alwashin gudanar da karba-karba.
— Tafiyar Mamman ta bar baya da kura
A yanzu, mutane sun fara kalubalantar fitar da ya yi zuwa Ingilar saboda wasu na ganin ya saba dokar hana tashin jirage zuwa kasar waje.
Idan ba a manta ba matar shugaban kasa, Aisha Buhari ma ta je Hadaddiyar Daular Larabawa don neman maganin ciwon wuyan da ta sha fama da shi.