Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Mista Haliru Nababa, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari ta kasa.
Tabbatar da nadin Nababa ya biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar kan harkokin cikin gida ya gabatar yayin zamanta na ranar Laraba.
- Bashir Dandago ya bayyana a kotu
- ‘APC na bukatar mulki na shekara 32 don inganta rayuwar al’umma’
- An yi wa mutum 215,277 rigakafin Coronavirus a Najeriya
Aminiya ta samu cewa Shugaban Kwamitin, Sanata Kashim Shettima mai wakiltar shiyyar Borno ta Tsakiya, shi ne ya gabatar da rahoton.
Shettima wanda ke zaman tsohon Gwamnan Jihar Borno, ya bayyana wanda aka nada a matsayin jajirtaccen mutum, wanda zai yi aiki tukuru wajen ciyar da hukumar gaba.
Ya ce babu wani koke da aka gabatar game da nadin Nababa don haka ya bayar da shawarar a tabbatar da shi.