✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tabbatar da karin mutum biyar masu cutar kurona a Najeriya

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayyar Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum biyar masu dauke da cutar Kurona a kasar a cikin sa’o’i 36. Hakan ya…

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayyar Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum biyar masu dauke da cutar Kurona a kasar a cikin sa’o’i 36.

Hakan ya sa adadin masu dauke da cutar yanzu ya kai mutum takwas.

Wata sanarwa da Ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter da safiyar ranar Laraba ta bayyana cewa, “Ministan lafiya Dakta E. Osagie Ehanire ya tabbatar da samun sabbin masu dauke da cutar Kurona su biyar…”

Tun da farko dai Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa [NCDC] ce ta tabbatar da hakan a ranar Laraba a shafinta na Twitter.

Mutum uku daga cikin sababbin masu dauke da cutar sun shigo ne daga kasar Amurka yayin da biyu suka shigo daga Birtaniya.

Biyu daga cikin mutanen da suka zo daga Amurka wata ’ya Najeriya ce da jaririnta dan makwanni shida.

Shi kuwa na ukun Ba’amerike ne da ya shigo ta kasa, lamarin da ya say a zama mai dauke da cutar na farko da ba ta jirgin sama ya shigo ba.

Sauran mutum biyun da aka samu suna dauke da cutar wadanda suka shigo daga Birtaniya ’yan Najeriya ne su ma.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa a sanarwar da aka bayar ranar Talata ta samun mai dauke da cutar wata ’yar Najeriya ce da ta dawo daga Birtaniya ranar 13 ga watan Maris.

Na biyu kuma wani bawan Allah ne wadanda ya yi mu’amala da mutum na farko da aka samu yana dauke da cutar, wato dan Italiyan nan da ya dawo daga Milan, ya sauka a Legas a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tuni dai hukumomi suka haramta wa matafiya daga wasu kasashe 13 shigowa Najeriya.

Kasashen sun hada da Amurka da Birtaniya da wasu kasashen Turai da na Asiya.

Bugu da kari, an rufe sansanonin masu yi wa kasa hidima bayan da aka dakatar da Gasar Wasannin Motsa Jiki ta Kasa don kauce wa yaduwar cutar.