Kasar Saudiya ta tabbatar da samun bullar cutar Kurona a karon farko daga wani dan kasar da ya dawo daga kasar Iran.
Mutun na farko da aka samu da cutar a Saudiyya ya shigo da ita ne bayan tafiya Bahrain da Iran. bayan wani gwajin da aka yi masa aka tabbatar da yana dauke da cutar.
Yan kwanakin da suka wuce ne Saudiyya ta dauki matakin dakatar da yan kasashen waje shiga kasar domin gudanar da ibadar Umrah a biranen Makkah da Madinah.
Saudiyya ce ta karshe wajen bullar cutar a cikin sauran kasashen Larabawa. An tabbatar da bullar cutar Kurona a Jordan da Tunisiya ranar Litini.
A makon da ya gaba ta ne Saudiyya ta dauki matakin dakatar da ‘yan kasashen waje shiga kasar domin gudanar da ibadar Umrah a biranen Makkah da Madinah, saboda gudun yaduwar cutar.