✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An soke shagulgulan Kirsimeti da na sabuwar shekara a Jihar Binuwai

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayar da sanarwar dakatar da shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar Shekara a jihar.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayar da sanarwar dakatar da shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar Shekara a dukkan kananan hukumomin Jihar 23.

Ya ce sun yanke shawarar ne a taronsu na Majalisar Tsaron Jihar da ya gudana a fadar gwamnatin jhar dake Makurdi.

A cewar sa, saboda tabarbarewar al’amuran tsaro a fadin jihar, Majalisar ta yanke shawarar dakatar da bukukuwan a fadin jihar.

Ortom, ya shawarci mutanen jihar da su gudanar da bukukuwan nasu a gidajensu tare da bin shawarwarin da hukumomin kula da lafiya suka bayar na dakile yaduwar COVID-19.

Gwamnan ya kuma shawar ce su da su bayar da rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba ga hukumar tsaro mafi kusa da su.