Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu sama da 500 a jihar saboda gazawarsu na bin sharudan ayyukan da ta gindaya musu.
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
- COVID-19: An bayyana ranar sake bude makarantu a jihar Legas
Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Ibrahim Abdullahi shine ya tabbatarwa da ’yan jarida hakan a Zamfara ranar Talata.
Ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta kaddamar da kwamitin kar-ta-kwana da zai tabbatar an aiwatar da umarnin rufe makarantun.
Alhaji Ibrahim ya ce za a kyale makarantun su sake budewa ne kawai idan suka bi dokokin da gwamnatin jihar ta gindaya musu.
“Dole ne a bi dokoki da ka’idojin da muka shimfida wa makarantun kafin mu dawo musu da lasisinsu su ci gaba da aiki,” inji shi.
Ya yi zargin cewa gwamnan jihar, Bello Matawalle ya tarar da tsari mara inganci inda ake bukatar makarantu masu zaman kansu su biya N30,000, wanda da zarar sun yi hakan shikenan gwamnati ba ta da damar sanya musu doka.
“Amma a yanzu haka, akwai wani daftarin doka da muke aiki a kai da kuma za mu aike wa Majalisar Dokokin Jihar wajen ganin an ba Ma’aikatar Ilimi ta jihar ikon kula da makarantu masu zaman kansu a jihar,” inji Kwamishinan.
Ya kuma ce tuni aka daga likafar sashen ma’aikatar ilimin da zai rika kula da makarantun masu zaman kansu zuwa cikakke kuma mai cin gashin kansa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.