Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta sanar da soke hawan da ta saba gudanarwa yayin shagulgulan bikin Babbar Sallah saboda kalubalen tsaron da ya addabi Jihar.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da masarautar ta aike wa dukkan masu rike da sarauta a cikinta ranar Talata.
- Gobara ta kashe mutum 64 a wurin killace masu COVID-19
- An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto
A cewar sanarwar, wacce Danejin Daura, Abdulmumin Salihu ya sanya wa hannu a madadin Sakataren masarautar, “Bayan gaisuwa da fatan alheri, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Dr. Umar Farouk Umar CON, ya umarceni da na sanar da kai cewa Babbar Sallah (Eid-el Kabir) ta kama ranar Talata, 20 ga watan Yulin 2020.
“Sakamaon haka, ana sanar da kai cewa ba za a yi hawan Sallah ba a dalilin yanayin da ake ciki na rashin tabbataccen tsaro da sauran abubuwan da suka addabi shugabanni da mabiyansu.
“A maimakon haka, za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba, bayan da aka kammala za a gudanar da addu’a ta musamman a Fadar Mai Martaba Sarki don samun dauwamammnen zaman lafiya, karuwar arziki da walwalar jama’a,” inji sanarwar.
Ko a Karamar Sallar da ta gabata dai Masarautar ta Daura da ma wasu da dama a Arewacin kasar nan ba su gudanar da hawan ba sakamakon kalubalen na tsaro.
Jihar Katsina dai na daga cikin Jihohin da ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da ma na ’yan bindiga ya ki ci ya ki cinyewa.