Gwamnatin Kasar Kamaru ta soke bukukuwan tunawa da zagayowar ranar samun ’yancin kasar a sakamakon yadda annobar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ofishin Sakatare Janar na Kasar, Ferdinand Ngoh Ngoh, ta ce Shugaba Paul Biya ya soke bukukuwan zagayowar ranar da kasar ta samu ’yanci a shekarar 1972.
- An sauya wurin da za a buga wasan karshe na kofin zakarun Turai
- Wajibi ne mu taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro — Sarkin Jema’a
Sanarwar ta ce Shugaba Biya yana kira ga ’yan kasar da su ci gaba da yi wa dokokin dakile yaduwar cutar Coronavirus biyayya a yayin bikin wanda ya fado a lokutan bukukuwan Karamar Sallah.
“Tabbas cutar Coronavirus gaskiya ce a yayin da kasar take ci gaba da kokari wajen ganin ta kawar da ita,” a cewar sanarwar.
A halin yanzu dai an samu mutum 74,949 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar yayin da tuni mutum 1,152 suka riga mu gidan gaskiya.