Kungiyar Injiniyoyi mata ta kasa reshen Jihar Kano ta shirya gasa tsakanin wasu makarantun sakandiren ’yan mata da ke fadin Jihar Kano, inda Makarantar ’Yan Mata ta Kano Capital ta sami nasarar lashe gasar.
kungiyar ta shirya wannan gasa ce a tsakanin makarantun sakandiren a kan darussan da suka shafi kimiyya, wadanda suka hada da lissafi da ilimin sanin halittu da sauransu.
Da take jawabi a wajen gasar, shugabar kungiyar ta injiniyoyi mata reshen Jihar Kano, Hajiya Amina Sallau Aliyu ta bayyana cewa kungiyar ta shirya wannan gasa ce don karfafa gwiwar yara mata don su ba darussan kimiyya muhimmanci, la’akari da yadda ake yi wa darussan ganin matsayin wasu masu wuyar fahimta. Ta ce bai wa ’ya’ya mata dama don yin zurfi a kwasa-kwasan kimiyya zai taimaka kwarai da gaske wajen ci gaban mata a Jihar Kano.
Su ma daliban da suka sami nasarar gasar sun shaida wa Aminiya farin cikinsu tare da mika godiyarsu ga kungiyar.
Makarantun da suka sami fafatawa a gasar sun hada da Kwalejin ’Yan Mata ta Dala da Makarantar Kano Kapital da kuma Makaranatar ’Yan Mata ta Shekara.