Ana cikin rudani game da matsayin makarantu a Karamar Hukumar Kajuru bayan sanarwar Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna cewa dukkan makarantun jihar su kasance a bude.
Wasika daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ta umarci a rufe daukacin makarantun da ke Karamar Hukumar Kajuru saboda karuwar matsalar tsaro.
- Saudiyya ta wajabta wa alhazai karbar rigakafin COVID-19
- ’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari
Ma’aikatar ta ba da umarnin ne kwanaki kadan bayan an sace dalibai da malamai a makarantar firamare ta UBE da ke kauyen Rama, daura da garin Birnin Gwari.
Da farko El-Rufai yayin jawabi bayan taron Majalisar Tsaron Jihar a ranar Talata, ya umarci daukacin makarantun jihar da su kasance a bude, sannan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na yin aiki tare da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalar rashin tsaro.
A ranar ce kuma Ma’aikatar Ilimin ta umarci Shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke Kajuru su rufe makarantun nan take.
Kajuru na daya daga cikin kananan hukumomi biyar da ke fuskantar kalubalen tsaro a jihar ta Kaduna.
Wasikar ta ce: “Sakamakon yawaitar sace-sacen mutane da sauran kalubalen tsaro a wasu garuruwa da kauyukan Karamar Hukumar Kajuru;
“Babban Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Makarantu na Kaduna ya umurce ni da in sanar da shugabannin makarantun gwamnati da masu masu zaman kansu a karamar hukumar da su rufe su nan take tun daga 16 ga Maris 2021.
“Babu makarantun da ya kamata su sake budewa har sai an umurce ku da yin hakan. Ku kasance masu kiyaye tsaro a kowane lokaci.”