✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci matasa su kaurace wa shaye-shaye

An bayyana cewa lalacewar tarbiyyar matasa a halin yanzuzu da kuma fadawa cikin shan miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyina asiri ya ta’allaka ne ga…

An bayyana cewa lalacewar tarbiyyar matasa a halin yanzuzu da kuma fadawa cikin shan miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyina asiri ya ta’allaka ne ga sakacin iyaye da rashin sanya ido a kan duk wata mu’amala da ’ya’yansu ke yi da kuma rashin matsa kaimi wajen ba su tarbiyya ingantacciya, wanda hakan ne ma ke haifar da wasun matasa na shiga kungiyoyi irin na ta’addanci daban-daban.
Sheik Muhammad Salisu Musa, malamin da kungiyar Izala ta kasa ta tura Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bayyana haka yayin amsa tambayoyin Aminiya, jim kadan da kammala taron yini guda domin fadakar da matasa illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyina ta’addanci da kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala ta kasa reshen Jihar Kurosriba ya gabatar karo na hudu a Kalaba, babban birnin jihar.
Da aka tambaye shi ko me addinin Musulnci ya ce game da illar shan miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyina ta’addanci? A nan sai malamin ya ce: “Allah madaukakin sarki Ya yi hani da wannan sannan kuma yau abubuwan da suke faruwa a duniyar matasa, yau an wayi gari wasu abokansu marasa kirki ne suke bata rayuwar abokan nasu, wanda lamarin ya kazanta domin ta nan ne ma ake samun wasu matasan na shiga kungiyoyi na asiri, wasu kuma suna shiga shaye-shayen tabar wi-wi da shalasha, musamman kwayoyin nan da ake amfani da su wajen yi wa marasa lafiya jinya. Sai matashi ya sha ya bugu, wanda sanadiyar hakan sai ta haifar masa da illa. Manzon tsira ya tabbatar da cewa dukkanin wani abu da zai sa hankali ya gushe, idan an sha shi ya haramta.”
Daga nan sai ya bukaci matasa da “lallai su dawo zuwa bauta wa Allah madaukakin sarki, su bar wannan kayan shaye-shaye na shalisho, na wiwi,  na kwayoyi. Daga nan ne kuma sai a koyi ta’addanci. To kungiyar Izala tana kira a daina irin wadanann abubuwan, duk babu kyau.” Ya danganta matsalar daga sakacin wasu iyaye wajen tarbiyyar ’ya’yansu, wani lokaci kuma daga malamai da suka kasance tare da matasan, rashin samun kyakkyawar tarbiya yakan jawo wannan. Ya ci gaba da cewa wani lokaci rashin aikin yi, musamman ga matasan da suka gama karatu, suka yi manya-manyan kwalejoji da kuma jami’o’i, suka gama ba su da aikin yi; sai su rika yanke shawarar shan miyagun kwayoyi domin su rage masu tunani da kuma yawan zullumi.
Da ya juya kan sakon da kungiyar Izala ta ce a isar wa al’umma dangane da kokarin warware wasu daga cikin matsalolin da wasu da suka yi mulki baya suka jefa kasar nan ciki, Sheik Salisu ya bayyana cewa kungiyar Izala dari bisa dari na goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da Gwamnatin Muhammadu Buhari take yi halin yanzu haka nan kuma a kowane mataki, talaka, dan kasuwa da kuma ma’aikata, kowa ya yi kokari ya gyara halayyarsa, domin ci gaban kasa da al’ummarta. A taimaka wa gwamanti, musamman Shugaban kasa, a taya shi da addu’a a wannan jan aiki da ya sanya a gaba na yaki da cin hanci da rashawa.