Tsohon mai tsaron baya na Chelsea, Frank Leboeuf, ya shawarci kocin Chelsea, Frank Lampard da ya yi gaggawar barin kulob din sakamakon rugujewar lamura.
Leboeuf ya nuna takaicinsa kan yadda kakar bana ta rikice wa Chelsea a duka gasanni da ta shiga.
- Barcelona za ta yi asarar kudin shiga saboda gyaran Camp Nou
- Mun cika da mamakin bajintar Haaland — Guardiola
Akalla dai ya cancanta Chelsea su nemi shiga hudun farko na teburin gasar Firimiya, saboda su samu damar buga gasar zakarun Turai ta badi.
Haka ya kamata, musamman ganin yadda sabon mamallakin kulob din, Todd Boehly, ya shirya sakin kudi don sayo ‘yan wasa.
Sai dai Chelsea sun sauko zuwa na 12 a teburin Firimiya, yayin da zuwa yau suka sauya mai horarwa har sau uku a wannan kakar.
Wannan ne ya janyon tsohon dan wasan Chelsea, Leboeuf yake cewa kocin wucin gadi, Lampard, ya gaggauta ajiye aiki a Chelsea, bayan yin rashin nasara a wasanni shida zuwa yanzu.
Leboeuf ya bayyana wannan ra’ayin nasa ga tashar ESPN, inda ya ce, “Babu abin da zan ce ga Frank Lampard, sai dai, ka yi ta kanka. Ka kama gabanka ba bata lokaci. Babu abin da za ka iya musu.”
Tsohon dan wasan wanda ya taba cin Kofin Duniya da kasar Faransa, ya kara da cewa, “Frank Lampard, ka kama gabanka saboda ba rike ka za a yi a nan ba. Kuma da wuya ka iya cin wasa har wannan kakar ta kare”.
A yanzu dai, tuni aka kori Chelsea daga Gasar Zakarun Turai, bayan buga wasa da Real Madrid a zagayen kusa da na karshe.
Wani abin ban tsoro shi ne, a wasanni biyar da suka rage musu a gasar Firimiya, za su kara da gaggan kungiyoyi kamar Manchester City da Manchester United da Newcastle.