✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sauke shugaban makaranta saboda ya ba dalibai hutun Sallah

Aminiya ta fahimci cewa, hakan ya saba da umarnin da gwamnatin Jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Sanusi Sa’id Kiru, ya bayar da lamunin sauke Shugaban Makarantar GSS Dambatta, Sabo Muhammad Ahmad daga mukaminsa.

An dai sauke shugaban ne saboda saba wa umarnin gwamnati na bai wa dalibai hutun Babbar Sallah.

Bayanai sun ce an tube shi ne sakamakon bayar da hutun ga dalibai 300 da ke zana jarrabawar kammala sakandire ta NECO.

Aminiya ta fahimci cewa, hakan ya saba da umarnin da gwamnatin Jihar ta bayar na ci gaba da tabbatar da zaman daliban a wannan lokaci.

A cewar Kwamishinan Ilimin, Sabo Muhammad ya bai wa daliban damar koma wa gidajensu, inda shi ma ya koma garinsu domin gudanar da bikin Sallah ba tare da sanar wa mahukuntan da suka dace ba.

“Wannan lamari ya nuna sakaci da halin-ko-in–kula gami da cin amanar da aka bai wa shugaban makarantar, kari a kan rashin da’a da biyayya ga umarnin gwamnati,” a cewar Kiru.

Kwamishinan ya kuma umarci shugaban makarantar da ya gabatar da kansa a Ma’aikatar Ilimin, inda daga nan kuma za a san mataki na gaba da za a dauka a kansa.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, za a maye gurbin Sabo Muhammad da wani babban jami’i a Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta Jihar.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin Jihar Kano ta umarci duk makarantun kwana a kan kada su bayar da hutun Sallah ga daliban da ke zana jarrabawar ta NECO.

A kan haka ne gwamnatin ta yi wa makarantun kyakkyawan tanadi na abinci, ciki har da sayen shanu 19 domin su yi shagalin Sallar a makaranta.

A cewar Kwamishinan, gwamnati ta yi wa daliban duk wani tanadi na gudanar da shagalin Sallah a makarantun cikin annashuwa da jin dadi.