‘Yan sanda a Jihar Legas suna ci gaba da tsare Dagacin Shangisha Cif Yusuf Ogundare, wanda ya yi garkuwa da kansa domin shafa wa Hakimin yankin kashin kaji. A daidai wannan lokaci ne su ma ‘yan sandan Jihar Oyo suka yi irin wannan kame na wata matar aure mai suna Bukola Ogun, wacce ta yi garkuwa da kanta tare da neman kudin fansa Naira miliyan 10 daga hannun mijinta da ke kasar Amurka.
Asirin Baale, wato Dagacin Shangisa Cif Yusuf Ogundare ya tonu ne a lokacin da jami’an tsaro suka kama shi a maboyarsa a Ibadan. Binciken da suka gudanar ya nuna cewa a ranar 5 ga watan da muke ciki (Yuli) ne basaraken ya hada baki da kanensa mai suna Mohammed Adams da suka bayar da sanarwar sace shi, tare da garkuwa da shi. ‘Yan sandan sun hanzarta daukar matakin tsananta bincike domin gano halin da yake ciki, tare da kubutar da shi daga hannun wadanda suka sace shi. Amma a binciken ne suka gano karyar Basaraken da ya yi garkuwa da kansa da nufin bata sunan Hakiminsa na yankin Shangisha da yake so ya shafa masa kashin kaji cewa da hannunsa wajen aikata wannan al’amari ta yadda zai kai ga tsige Hakimin daga sarauta domin Dagaci wato Baale Yusuf Ogundare ya samu hayewa bisa karaga.
..Gwamna Ambode ya sauke Dagacin Shangisha Cif Yusuf Ogundare daga karaga a dalilin abin kunyar da ya aikata na yin garkuwa da kansa domin shafa wa Hakimin Magodo kashin kaji da jefa gwamnati cikin halin damuwa. Bayanin tube Basaraken daga mukaminsa yana kunshe ne cikin takardar sanarwa da Kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya na Jihar Legas Mista Muslim Folami ya sanya wa hannu, cewa: “Muna sanar da dukkan jama’a cewa Gwamna Akinwunmi Ambode ya bayar da umarnin tube Baale na Shangisha Cif Yusuf Mutiu Ogundare daga karaga da tuhumarsa gaban kotu ba tare da bata lokaci ba.” Sashe na 38 dakin baka na 1 na dokar sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya a Jihar Legas ya amince da Gwamna ya dakatar ko tube kowane Sarki da aka nada kafin a kafa dokar ko bayan an kafata .
Da yake nuna wannan Basarake da kanensa ga ‘yan jarida Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas Mista Fatai Owoseni ya ce, hadin gwiwar da aka samu a tsakanin ‘yan sanda da jami’an tsaro na DSS ne ya kai ga nasarar kama shi bayan kwanaki shida.
‘Yan sandan za su ci gaba da tsare Cif Yusuf Ogundare da kanensa Mohammed Adams da matarsa da aka tabbatar da cewa, sun hada baki ne suka kulla wannan makirci, a cewar Kwamishinan. Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa, kafin aukuwar wannan al’amari, akwai mummunar rashin jituwa a tsakanin wannan dagaci da hakiminsa.
A Jihar Oyo ma ‘yan sanda ne suka kama wata matar aure mai suna Bukola Ogun, wacce ta hada baki da wasu mutane da suka bayar da sanarwar saceta da garkuwa da ita, tare da neman kudin fansa Naira miliyan goma daga hannun mijinta da ke zaune a kasar Amurka. Jim kadan da samun labarin garkuwa da matarsa sai mijin nata daga Amurka ya bugo waya ga ‘yan sandan ya sanar da su, tare da neman su ceto masa matarsa.
Da yake nuna wannan mata da abokan huldarta su biyu ga ‘yan jarida Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude ya ce, al’amarin ya auku ne da yammacin ranar talata 4 ga watan Yuli a lokacin da wasu mutane su 3 suka shiga cikin gidan wannan mata a Ibadan suka sace ta tare da yin garkuwa da ita a wani wuri. “Bayan awa 4 da aukuwar al’amarin ne wadanda ake zargin suka buga wa mijin matar waya da neman kudin fansa kafin su sako matar. Ba tare da masaniyar cewa matarsa ce ta kitsa batun garkuwa da ita mijin nata ya yi rahoton lamarin ga ‘yan sanda. Ba tare da bata lokaci ba jami’an tsaro na rundunar yaki da fashi da makami SARS suka bazama wajen neman mutanen da suka sace wannan mata.”
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce, an yi nasarar kama mutane biyu da suka yi bayanan amincewa da bakinsu yadda matar da kanta ta kitsa wannan al’amari. Wadannan mutane su ne suka nuna wa jami’an tsaro wurin da matar ta boye kanta a cikin wani Hotel da ke Imalefealafia.
Bayan nuna ta ga ‘yan jarida Uwargida Bukola Ogun mai shekaru 37 da ‘ya’ya 2 ta yi nadamar abun da ta aikata.
“Ni ce na kitsa haka da kaina kuma na aikata haka ne domin ina so mijina ya dauke ni ya mayar da ni Amurka, inda yake zaune. Na san cewa ba zai iya biyan kudin fansa naira miliyan 10 da aka nema daga hannunsa ba amma idan da mun yi nasara to akwai tsarin yadda zan kubuta daga hannun wadanda suka sace ni wanda zai sa mijin nawa ya ji tsoron bari na a Ibadan ya kai ni Amurka mu ci gaba da zama tare,” inji ta.