✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sassauta wa dan kwallon Chelsea Matic hukuncin jan kati

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta sassauta hukuncin da ta kakabawa dan kwallon Chelsea Nemanja Matic na dage shi daga yin wasanni uku bayan…

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta sassauta hukuncin da ta kakabawa dan kwallon Chelsea Nemanja Matic na dage shi daga yin wasanni uku bayan alkalin wasa ya ba shi katin kora a wasan da kulob din ya yi da na Burnley a gasar rukunin firimiya ta Ingila a ranar Asabar da ta wuce.

Shi dai Matic ya samu katin korar ne bayan ya tunkude dan kwallon Burnley Ashely Barnes da yi zargin ya nemi ji masa ciwo da gangan ne a wata keta da ya yi masa. An tashi wasan ne da ci 1-1.
Yakamata a ce Matic ba zai yi wasanni uku ba ne amma bayan da Hukumar ta FA ta yi nazarin wasan, sai ta rage masa hukuncin ya koma wasanni biyu.
Sai dai wannan hukunci bai yi wa kulob din Chelsea dadi ba, don tuni kulob din ya fitar da wata sanarwa a shekaranjiya Laraba inda ya nua bacin ransa a kan matakin da Hukumar ta dauka. Kulob din ya ce dan kwallonsu Matic ya tunkude Ashley Barnes ne saboda muguwar ketar da ya yi masa, kuma bacin raine ya sa shi aikata haka, don haka wasa daya kacal yakamata a ce dan kwallon ba zai yi ba, ba wasa biyu ba.
Yanzu Matic ba zai buga wa Chelsea wasan karshen da za ta yi da kulob din Tottenham a gasar cin kofin Carling na Ingila da za a yi jibi ba.