Gwamnatin Jihar Bauchi ta sassauta dokar hana fita na awanni 24 da aka sanya a Karamar Hukumar Katagum.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ta ce “Da ga yanzu dokar za ta soma aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Sannan ta bukaci mazauna yankin da su cigaba da biyayya ga matakan da gwamnatin take ɗauka wajen dawo da doka da oda a yankin.
Kashim ya ce, “Majalisar tsaron jihar Bauchi ta yi nazarin dokar da aka sa kuma ta yi la’akari da yadda ake samun dawowar zaman lafiya a cikin garin Azare da kewaye na Karamar Hukumar Katagum.
- DAGA LARABA: Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi
- Yadda aka kama ƙasurgumin ɗan fashi da makami a Kano
Don haka ta, “ta amince da sassauta dokar hana fita da aka kakaba wa yankin,”
Tun da farko an sanya dokar hana fita ne, bayan tashe-tashen hankula da aka samu a yankin yayin zanga-zangar da aka gudanar na neman kawo karshen yunwa wanda ta rikiɗe zuwa tarzoma da lalata kayan gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane a garin Azare.