Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai tare da buƙatar jihohi su gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
- Ambaliya ta yi barna a jihohi 20, wasu 13 na cikin hadari
- ’Yan bindiga sun harbe manomi, sun sace matansa a Kaduna
A baya-bayan nan, Gwamnatin Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana aniyar gwamnatin na gudanar da zaɓen nan ba da jimawa ba.
A wani taron manema labarai, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya tabbatar da shirinsu na gudanar da zaɓen.
Ya kuma bayyana cewa za a yi wa dukkanin ‘yan takara gwajin miyagun ƙwayoyi kafin a ba su damar tsayawa takara.
Jadawalin zaɓen zai kasance kamar haka:
– Zaɓen fidda gwani na jam’iyyu da gabatar da bayanan ‘yan takara: 6 ga watan Satumba zuwa 18 ga watan Oktoba.
– Fitar da sunayen ‘yan takara: 25 ga watan Oktoba.
– Ranar ƙarshe da jam’iyyu za su sauya sunayen ‘yan takara: 1 ga watan Nuwamba.
Zaɓen ƙananan hukumomi na ƙarshe a Kano an gudanar da shi ne a ranar 16 ga watan Janairu, 2021 a faɗin ƙananan hukumomi 44 da mazaɓu 484.
A halin yanzu, waɗannan ƙananaa hukumomi na ƙarƙashin jagorancin shugabannin riƙon ƙwarya.
Hukumar zaɓen ta kuma sanar da cewa haramun ne manna fastocin yaƙin neman zaɓe a ginin gwamnati, fada, da wuraren ibada, kuma za ta hana duk wanda ya keta wannan doka tsayawa takara.