Gwamnatin Jihar Edo ta sanya dokar takaita zirga-zirga ta tsawon sa’a 24 a garuruwan Obazagbon zuwa Ogheghe, da ke kusa da kauyen Irhirhi-Arogba-Obazagbon-Ogheghe.
Gwamnatin ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 29 zuwa Juma’a 30 ga watan Satumba da muke ciki.
- Damfarar masu neman aiki ta kai Daraktan Gwamnatin Sakkwato kurkuku
- NAJERIYA A YAU: Shin Rikicin Manyan Jam’iyyu Zai Amfani Masu Tasowa A Zaben 2023?
“Gwamnati na gudanar da aikin tsaro a yankin, kuma tana gargadin al’umma da su kaurace wa titin Obazagbon zuwa Ogheghe daga ranar 29 ga Satumba zuwa 30, don kada su jefa rayuwarsu a hadari.
“Da haka muke shawartar mazauna wuraren, da su zauna a gida, har zuwa lokacin da za a kammala,”, in ji Gwamnatin.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar, mai dauke da sa hannun Sakatarenta, Osarodion Ogie, ta kara da cewa duk wanda ya shiga hannnu kan karya dokar, zai fuskanci hukunci.