✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya dokar takaita zirga-zirga a Birnin Gwari

An sanya dokar takaita zirga-zirga a Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna bayan ’yan bindiga sun yi wa garin kawanya.

An sanya dokar takaita zirga-zirga a garin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna bayan ’yan bindiga sun yi wa garin kawanya.

Daya daga cikin dattawan garin kuma Danmasanin Birnin Gwari, Zubairu Abdulrauf, ya shaida wa Aminiya cewa, bayan harin ’yan bindiga tsakiyar garin ne shugaban karamar hukumar, Abdullahi Ibrahim Amir, ya ba da umarnin takaita zirgi-zirgga a cikin garin.

Sanarwar da kakakin shugaban karamar hukumar, Mustapha Idris Abdulra’uf, ya fitar ta ce “An hana fita da keke ko babur a daukacin garin Birnin Gwari daga 8:30pm na daren 26 ga watan Mayu, 2023.

“An hana zirga-zirgar mota daga karfe 9:30pm sannan an zirga-zirga na kafa daga karfe 10:pm dare; Don haka duk wanda jami’an tsaro suka kama da karya daya daga cikin dokokin nan to ya kuka da kansa,” in ji shi.

Mustapha ya kuma shaida wa mazauna garin cewa an dauki matakin ne saboda kare rayuka da dukiyoyin mutane, ba don a matsa masu ba.

’Yan bindiga sun yi wa Birnin Gwari kawanya

Mazauna Birnin Gwari dai sun koka a kan yadda ’yan bindiga suka yi wa garin kawanya a ’yan kwanakin nan.

Sun bayyana cewa ’yan fashin dajin sun fara shigowa tsakiyar garin suna yin sata da garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, wanda bai taba faruwa ba a cikin garin

Danmasanin Birnin Gwari, Zubairu Abdulrauf, ya tabbatar wa Aminiya faruwar irin haka a ’yan kwanakin nan ’yan bindigan sun mamaye garin, musamman wayanda suka gudo daga Jihar Zamfara.

“Na fadi cewa fa ’yan bindingan nan sun yi wa garin Birnin Gwari kawanya don haka jami’an tsaro su dauki mataki.

“Amma ina, sai ga shi har sun fara shiga tsakaiyar gari suna daukar mutane, abin a da bai tana faruwa ba,” in ji shi.

Ya ce wadanda aka sace kwana biyu da suka wuce a unguwar Gobirawa suke da zama kuma ba su da nisa da tashar talabijin na NTA Birnin Gwari.