✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomi 3 a Yobe

Gwamna Buni ya yaba wa matasan da suka janye daga shiga zanga-zangar matsin rayuwa a jihar.

Gwamnatin Yobe ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a ƙananan hukumomi uku na jihar.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Potiskum, Nguru, da kuma Gashua.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mashawarcin gwamnan jihar na musamman kan harkokin tsaron, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya ya fitar a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce ɗaukar matakin ya zama tilas la’akari da yadda wasu ɓata-gari ke fakewa da zanga-zangar matsin rayuwa suna sacewa da lalata kadarorin jama’a da na gwamnati.

Abdulsalam ya ce a yayin da ake umartar jami’an tsaro da su tabbatar an kiyaye dokar, yana kuma shawartar jama’ar ƙananan hukumomin da su zauna a gida domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kazalika, Gwamna Mai Mala Buni ya yaba wa al’ummar jihar musamman matasan da suka amsa kiran janyewa daga zanga-zangar matsin rayuwa la’akari da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar.