An samu mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Kano ranar Asabar.
Wata majiya ta nuna cewa mutumin da ya kamun wani babban mutum ne da ya koma Kano daga Legas.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Tsanyawa ya ba da tabbacin faruwar lamarin, sai dai ya ki yin karin haske game da mutumin da ya kamu.
Ana sa ran gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai yi wa jama’ar jihar bayani game da lamarin nan ba da jimawa ba.