✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu mutum na biyu da ya kamu da cutar Kurona a Najeriya

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da samun mutum na biyu da ya kamu da cutar Kurona (COVID19), a Najeriya. Dakta Osagie, ya bayyana…

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da samun mutum na biyu da ya kamu da cutar Kurona (COVID19), a Najeriya.

Dakta Osagie, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a garin Benin babban birnin jihar Edo lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a asibitin koyarwa na jami’ar Benin (UBTH).

Ministan ya kara da cewa, bullar cutar ba wai an sake shigon da ita kasar bane, amma wanda ke da cutar makusanci ne ga dan kasar Italiyan nan da ya shigo da cutar kasar.

Mutumin na biyu mai dauke da cutar Kurona ya samu cutar ne daga wannan dan kasar Italiyan, a yanzu haka an killace direban da ya dauko dan kasar Italiyan.

A kwanakin baya ne aka killace mutum 40 a jihar Ogun yayin da aka killace mutum 20 a jihar Legas, wadanda suka yi hulda da dan kasar Italiyan

Ministan, ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da biciken sauran mutanen da suka yi alaka dan kasar Italiyan.

Gwamnati ta ware kusan Naira biliyan 1 don rigakafn yaduwar cutar Kurona.