’Yan sanda sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi ’yan bindiga ne bayan wata musayar wuta da suka yi a kauyen Maina-Maji da ke Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Cikin wadanda suka shiga hannun har da wani matashi mai shekaru 20, dauke da kudin fansar da suka karba Naira miliyan 8.4 da bindigu da harsasi 92 da wayoyin salula guda takwas.
Da yake holen wadana ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Umar Mamman Sanda ya ce kalubalen tsaro na kara dabaibaye jihar, wanda ya sa dole su kara tsayuwar daka domin kawo karshensu.
“Laifuka irinsu cin zarafin mata da na dabanci da fashi da makami da satar mutane, hadi da sauran manyan laifuka, sun mamaye jiharmu a baya-bayan nan.
“A ranar 7-9-2022, jami’anmu da ke ofishin Maina-Maji sun gudanar da sintiri, kuma da gudummawar ’yan bijilanti sun samu nasarar kamo wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne da ke fashi da makami da satar shanu a kauyukan Kananan Hukumomin Alkaleri da Dass da Tafawa Balewa da Bogoro da Toro da wani bangare na Jihar Filato.
“A wani samamen kuma, mun kamo wasu mutane shida a kauyen Sabon-Gida da ke Karamar Hukumar Tafawa Balewa da wasu a Karamar Hukumar Guram Wase da ke Jihar Filato.
“Wadanann mutane ana zarginsu da aikata laifin hadin baki wajen satar mutane da fashi da makami da satar shanu a kauyukan Alkaleri da Dass da Tafawa Balewa da Bongoro da Toro,” a cewar CP Sanda.
Kazalika, ya ce an samu bindiga kirar AK47 da alburusai 30 da kuma wata karamar bindiga mai dauke da harsasai 581 a hannun a ababen zargin.