✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu gobara sau 767 a Zamfara a 2020

Ba a taba samun yawan gobara haka ba a shekaru 10 da suka gabata

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara ta ce an samu gobara sau 767 a fadin Jihar a shekarar 2020.

Mukaddashin Daraktan Hukumar, Abdullahi Jibbo, ya ce ba a taba samun yawan gobara irin yadda aka samu 2020 a jihar ba cikin shekaru 10 da suka wuce.

Da yake bayani a Gusau a ranar Alhamis, Abdullahi Jibo, ya ce yawancin gobarar sun tashi ne sakamakon sakaci da kayan laturoni da kuma kin bin ka’idojin kare aukuwar gobara a gidaje da wuraren kasuwanci.

Ya ce Gusau ita ce Karamar Hukumar mafi yawan gobara a shekarar inda aka samu 237, Kaura Namoda 116; Talata Mafara 112; Tsafe 85 sai Gummi, 77.

Ya shawarci jama’a su guji yin abubuwan da ke iya haddasa tashin gobara, hukumomi kuma su tabbatar da bin matakan kare aukuwarta a dukkannin kasuwanni.

Abdullahi ya kuma gargadi mutane su guji ajiye kayan fetur a gidajensu, inda ya ce jami’an hukumar na zagawa a Jihar domin tabbatar da ana bin dokokin kare aukuwar gobara, musamman a wuraren kasuwanci.

Sauran kanan hukumomin Jihar Zamfara da aka samu gobarar a cewarsa su ne: Anka 56, Shinkafi 36, Bungudu 32, Maru 28, Bakura ma 28 sai kuma Nasarawa 13.

An samu 11 a Birnin Magaji, 10 a Maradun, Jangebe 10, Kasuwa Daji 10 , Zurmi 8, Dansadau 6 sai kuma Bukkuyum 4.