A farkon makon nan an fara samun dogayen layukan man fetur a wasu gidajen mai da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kodayake rahotanni daga Jihar Legas suna cewa matsalar karancin man ta fara gushewa a can, amma wani dillalin mai, ya ce abin da ya haddasa dogayen layukan ba ya rasa nasaba da fargabar da kuma tsoro kada halin da ake ciki a Legas ya karaso Abuja. Wannan ya sa jama’a suke gaggawar sayan mai.
A ranar Litinin ne Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa ya tura tankokin mai Abuja don magance matsalar dogayen layukan man wadda zaben cike gurbin da Hukumar Zabe (INEC) ta gudnar a Jihar Neja ya haddasa saboda dakatar da rarraba shi daga defot din garin Suleja. Kamfanin ya ce ya kara adadin da yake bai wa garin Abuja daga tanka 160 a rana zuwa 250.
A karshe kamfanin ya bukaci jama’a da su guje wa boye mai da kuma karkatar da shi saboda a cewar sanarwar, kamfanin a shirye yake na wadata Abuja da kuma garuruwan da ke kewaye da ita da mai.
An samu dogayen layukan mai a Abuja
A farkon makon nan an fara samun dogayen layukan man fetur a wasu gidajen mai da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.Kodayake rahotanni daga Jihar Legas…