Wani rahoto da kafar sadarwar BBC ta fitar ya nuna an samu dan kwallon da ya fi Usain Bolt gudu a Ingila. Rahoton ya nuna dan kwallon ya zarce Usain Bolt mutumin da ake ganin babu kamarsa wajen gudu a duk fadin udniya a halin yanzu. Rahoton ya nuna dan kwallon kulob din Arsenal mai suna Hector Bellerin ne ya wuce Bolt da kimanin mita 40. Sai dai wannan rahoto hasashe ne, tun da ba a taba gwada su a zahiri an tabbatar ba.
Rahoton ya cigaba da cewa, da za a gwada dan tsere Bolt da dan kwallo Bellerin ana ganin Bellerin ne zai wuce Usain Bolt da tazarar mita 40.
Usain Bolt wanda ya kafa sabon tarihi a gasar tsere ta duniya a shekarar 2009, ya yi gudun mita 100 ne a tsakanin minti 9 da dakika 58 al’amarin da ya sa ya kafa sabon tarihi.
Sai dai Bellerin, dan kimanin shekara 21 haifaffen Sifen ya nuna shakkunsa a kan zai iya doke Usain Bolt a tseren mita 100 idan suka gwada su.
Usain Bolt ya nuna idan har ya yi ritaya daga yin gudu babu abin da ya fi sha’awa da ya wuce kwallon kafa. Hakan ce ta sa ya kai wa kulob din Manchester United na Ingila ziyara a lokacin da tsohon Koci Sa Aled Ferguson yake horarwa.
An samu dan kwallon da ya fi Usain Bolt gudu?
Wani rahoto da kafar sadarwar BBC ta fitar ya nuna an samu dan kwallon da ya fi Usain Bolt gudu a Ingila. Rahoton ya nuna…