Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Borno ta sanar da ɓullar cutar amai da gudawa ta kwalara a jihar.
Da yake bayyana hakan a cibiyar da ke sa ido a Maiduguri, Kwamishinan Lafiyar jihar, Farfesa Baba Gana, ya ce daga cikin samfura ɗari biyu da aka aika domin gudanar da gwaji, goma sha bakwai na ɗauke da ƙwayoyin cutar.
- Halin da iyalai ke ciki bayan mutuwar magidanta a hastarin kwalekwalen ’yan Maulidi
- Tifa ta take magidanci da iyalansa 6 a Zamfara
A cewarsa, an samu bullar cutar ce a sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta auku a bayan nan a jihar.
Farfesan ya bayyana wuraren da cutar ta ɓulla da suka haɗa da Jeere da Mafa da Konduga, Dikwa da kuma MMC.
Duk da yake ba a samu rahoton mutuwa ba, Kwamishinan ya ce ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙananan hukumomin da dama, musamman ma a daidai lokacin da ake samun ɓullar cutar a jihohin Adamawa da Yobe da ke maƙwabtaka da su.
Ya ce, kimanin mutane 451 aka yi zargin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomin daban-daban, amma 17 ne kawai aka tabbatar suna ɗauke da ƙwayoyin cutar.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ba da sanarwar ɗaukar matakin gaggawa don shawo kan wannan lamari, a yayin da ake ci gaba aikin haɗin gwiwa da hukumomin jin ƙai kamar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Médecins Sans Frontières (MSF) wajen samar da kayan agaji don kula da waɗanda abun ya shafa.
Ya kuma ce an samar da alluran rigakafi kusan 400,000.
Ana iya tuna cewa, a makon nan ne Gwamnatin Borno ta taƙaita bikin murnar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai, inda ta buƙaci ‘yan jihar da su duƙufa da yin addu’o’i.