Ranka ya dade ko za ka iya fada mana yadda tarihin Taura yake?
Taura tsohon gari ne mai dogon tarihi na shekaru aru-aru. Kuma sama da shekara 40 aka fara nada Hakimai a garin Taura wanda ya kawo ni ke yin hakimici a halin yanzu, kuma an fara nadin hakimai ne tun daga kan Hakimi Wakili Inuwa
Yaya za ka kwatantata karfin sarauta a baya da yanzu?
Yanzu an samu sauyi sosai wajen yadda ake gudanar da sarauta sabanin baya da sarakuna suke da karfi da iko, domin su ne da kotuna da alkalai kuma suke da wukar yanka. Kowa yana tsoronsu saboda duk abin da za su yi suna amfani ne da Littafin Allah Mai girma wajan zartar da hukunci saboda mafiya yawan sarakunan malamai ne, sun san Allah kuma suna aiki ne da Alkur’ani. Yanzu kuma siyasa ta lalata komai, an rage wa sarakuna karfi an rage musu karfin iko sabanin yadda suke da shi a baya da koda Shugaban karamar Hukuma ba ya da abokin aiki sai Hakimi ko Sarkin yankin, yanzu kuwa suna da kansiloli wadanda su ne abokan shawararsu sabanin yadda al’amura suke a baya da suke shawara da masu rike da sarautu.
Me ya sa darajar sarakuna ke raguwa a wajen talakawa da sauran al’ummar gari?
Ba wani abu ba ne ya sa darajar sarakuna take raguwa a wajen magoya baya ko sauran al’ummar gari illa rashin adalci da kwadayi. Duk Sarkin da ya zama mai kwadayi ko mara adalci a wajen talakawansa, dole martabarsa da kimarsa su ragu a wajen al’ummarsa
Ka ga kamar mu a nan masarautar Taura ba mu da aiki kullum sai neman yadda za mu taimaka wa al’ummarmu, mu kyautata musu, wannan shi ne babban burinmu kuma mu kwata wa duk wanda aka zalunta hakkinsa. Domin ba za mu amince da zalunci ba, wannan shi ne ya sa kullum muke da kima da martaba a idon mutanenmu. Allah Ya sani ba ma neman komai a wajen talakawanmu sai dai goyon bayansu kan yadda za mu ciyar da yankinmu gaba.
Dagatai nawa masarautarka ta Taura take da su?
Masarautar Taura tana da dagatai 13 da masu unguwanni 101, kuma muna da Limaman Masallatan Juma’a 22 da makarantun Islamiyya 87.
Kana da shekara nawa ka hau sarautar Taura?
Ina da shekara 40 aka nada ni Hakimin Taura. Yau shekaruna 50 a duniya shi ya sa ma yau nake yin bikin cika shekara goma a kan sarautar Hakimin Taura. Wannan hawa ne da ake yin sa domin sada zumunci tsakanin al’ummar garin Taura domin duk inda dan Taura yake a duniya, idan dai yana raye, yakan yi kokarin halartar wannan gagarumar hawa da muke yi duk shekara. Wani lokaci muna yin bikin ne a watan Janairu wani lokacin kuma muna yi ne a watan Disamba ba don komai ba sai don mu ba al’ummar Taura damar halartar bikin.
Ka taba yin nade-nade daga hawanka zuwa yanzu?
Gaskiya na fara nade-nade a masarautata, na yi guda bakwai a bana, kuma shekara biyar baya na nada mutane goma a kan matakan iko daban-daban. Na yi haka ne da nufin su rika taimaka min wajen gudanar da mulki saboda komai yana bukatar shawara, domin hannu daya ba ya daukar jinka, inji Bahaushe
Na yi nade-naden ne domin su rika taimaka min wajen warware matsalolin masarauta, duk bangaren da ka sani na nada wakili mai kula da bangaren saboda a rika taimaka min.
Yaya yanayin wannan hawa naka yake?
Ina tabbatarwa duk Jihar Jigawa babu Hakimin da yake shirya hawa bayan Mai Martaba Sarki ya gudanar da nasa hawan kamar nawa da nake shiryawa a nan masarautar ta Taura,
Mece ce babbar al’adar mutanen Taura?
Al’adarsu ita ce shadi da kokawa da dambe da kuma hawan kaho ta fuskar wasan gargajiya ke nan, kuma ba su da wata sana’a da ta wuce noma da kiwo.
Yaya batun iyali fa?
Ina da mata biyu da ’ya’ya 13.
Dukan masarautu ana yi musu kirari, ko mene kirarin Taura?
Ana yi wa Taura kirari ne da Taura ta dan Bilkassim, Taura mai mashiga daya, Taura garin malamai, Taura mai kamar Masar daga nesa tsintsiya madaurinku daya.
Me ya sa ake kiran garin da suna Taura?
Garin Taura ya samo asali ne daga cikin sunan wani shahararren malami masanin Attaura da ake kira Malam Mai Attaura. Malami ne da ya shahara a Jihar Kano, shi ne ya fito daga birnin Kano ya kafa garin Taura saboda irin ci gaban da ya samar a garin, shi ne aka yi amfani da sunansa ake cewa garin Taura maimakon a ce garin Mai Attaura.
A wata ruwayar kuma an ce ainihin wadansu mutane ne da suka kafa tudun Dala a Kano suka kafa Taura bayan sun yi shekara sama da 70, sai suka yi kaura suka koma birnin Kano shi ne suka kafa Tudun Dala da ke birnin Kano a halin yanzu.
Kuma abin da ya sa ake wa Taura lakabi da ta dan Bilkkassim shi ne saboda shi malami ne da ya shahara wajen yaki, ya yi kokari matuka wajen kare garin Taura daga hare-haren mayaka irin na wancan zamanin kuma saboda jarumtarsa ne al’ummar lokacin suka zabe shi a matsayin sarkinsu.
Amma a wata ruwayar kuma wai wani malami ne jarumi da ya shahara a tsakanin Kano da Daura da Lardin Gumel da Hadeja wadda ake cewa Dadi wanda ya zo daga kasar Daure, shi ne Sarkin Taura na farko tun kafin Jihadin Shehu Usman dan Fodiyo, an ce shi ne ma ya kafa garin Taura kamar yadda masana tarihi suke fada Sarki Dadi yana cikin jerin sarakunan Taura.
Garin Taura yana da ganuwa ne?
Garin Taura yana da ganuwa da kofofi kamar yadda sauran masarautu suke da su, kuma an yi mata Hakimai ne tun daga 1921 zuwa 1944 ciki har da dan Maje wanda shi ne Hakimin Taura na yanzu.
Ko za ka iya fada mana hakiman Taura?
Akwai dan Maje Zakari Ya’u da Magajin Malam Adamu Nachedi, da dan Isah Ummaru da Wakili Inuwa dan Indo da Magajin Malam Sani Yola, kuma a nan garin Taura ban da waje ina da masu unguwa 10.
Su ake kira dagatai ke nan kafin nada hakimai?
Su ne ake cewa sarki a da. A baya Taura su ne suka fara sarauta daga kan Sarki Dadi sai Sarki Manga sai Chaffatu sai Sarki Hukussiya da Sarki Barde kafin shigowar zamani. Sarki Dadi ya yi mulki ne a 1802 zuwa 1819 ka ga tun kafin zuwan Turawa ke nan, shi kuma Sarki Manga ya yi nasa mulkin daga 1819 zuwa 1826, Chaffatu kuma daga 1826 zuwa 1832, shi kuma Hukussiya daga 1832 zuwa 1842 sai Barde daga 1842 zuwa 1849.
Zuwa yanzu Taura ta yi hakimai nawa ke nan kuma sarakuna nawa?
Za a iya cewa ta yi hakimai bakwai ke nan kuma ta yi sarakuna 17 tun daga kan Sarki Dadi wanda ya fara mulki tun zamanin Turawa zuwa kan Sarki Musa Yamusa a 1945.