✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An same shi da kokon kan mutum a Ibadan

A ranar Talatar da ta gabata ce aka gurfanar da wani mutum dan shekara 30 mai suna Shehu Gidado a gaban Babbar Kotun Majistare da…

A ranar Talatar da ta gabata ce aka gurfanar da wani mutum dan shekara 30 mai suna Shehu Gidado a gaban Babbar Kotun Majistare da ke yankin Iyaganku, Ibadan, sakamakon samunsa da aka yi da kokon kai da hakarkarin mutum.

Gidado, wanda ke zaune a unguwar Iba New Site, Okokomaiko, Jihar Legas, an tuhume shi ne da laifin mallakar kokon kan mutum. dan sanda mai gabatar da kara a kotun, Sufeto Sunday Fatola, ya shaida wa kotun cewa, a ranar 7 ga watan Agustan bana, da misalin karfe 2:30, aka samu mutumin da ake tuhuma da kokon kan mutum a kan titin Ogbomoso zuwa Ilorin. Haka kuma an tuhumi mutumin da cewa an same shi da wasu hakarkarin mutane biyu daban-daban a tare da shi.

Fatola ya shaida wa kotun cewa ’yan sanda masu aiki a hanya ne suka tsaida wata motar haya, inda suka samu wanda ake tuhuma da wadannan sassan jiki na mutum kunshe a cikin wata bakar leda. “An samu wadannan kayayyaki da ake zargin cewa sassan jikin mutum ne kunshe a cikin leda a tare da Gidado, kuma ya kasa bayar da gamsasshen bayanin yadda aka yi ya same su,” kamar yadda mai gabatar da kara ya shaida wa kotu.

dan sandan ya bayyana cewa wannan laifi ya saba wa sashi na 329 (1) na CCP 38, Mujalladi na II na Dokokin Jihar Oyo, 2000.

Gidado dai ya musanta aikata laifin, inda Babban Majistare, Mista Abdulateef Adebisi ya amince da bayar da shi beli a kan Naira dubu 200 tare da mutum biyu masu tsaya masa. Daga bisani kuma ya daga shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba mai zuwa, domin ci gaba da sauraren shaidu.