✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako wakilin jaridar Punch da wasu mutum 2 da aka sace a Abuja

Ma'aikacin jaridar Punch, Okechukwu Nnodim da aka sace ranar uku ga watan Fabrairun 2021 da wasu mutum biyu

Ma’aikacin jaridar Punch, Okechukwu Nnodim da aka sace ranar uku ga watan Fabrairun 2021 da wasu mutum biyu a gidajensu dake Kubwa a Babban Birnin Tarayya Abuja sun kubuta.

Matar dan jaridar, Oluchi Nnodim ce tabbatar da sako su a ranar Lahadi, inda ta ce an sako mijin nata ne da tsakar daren ranar Asabar.

Ta ce mijin nata ya kubuta ne tare da sauran mutum biyun da aka sace.

Oluchi ta ce, “Miji na ya dawo tsakar dare amma har yanzu yana bacci.

“Lafiyarsa kalau, na kuma gode Allah da ya sa makiyanmu ba su yi mana dariya ba.

“Na godewa Allah da wannan baiwar da ya yi mana,” inji matar.

Ta kuma godewa dukkan wadanda suka bayar da gudummawa har mijin nata ya sami kubutar.

Dan jaridar dai da wasu mutane biyun da aka sace sun shafe kwanaki uku a hannun masu garkuwar bayan an sace su daga gidajensu ta karfin tsiya bayan harbe-harbe.

Tun da farko dai masu garkuwar sun bukaci a basu Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar dan jaridar.