✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako matar tsohon Shugaban Majalisar Edo

’Yan bindiga sun sako matar tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Zakawanu Garuba wadda suka yi garkuwa da ita ’yan sa’o’i bayan rasuwarsa a ranar…

’Yan bindiga sun sako matar tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Zakawanu Garuba wadda suka yi garkuwa da ita ’yan sa’o’i bayan rasuwarsa a ranar Asabar.

Rahotanni sun tabbatar da an sako Hassana, matar marigayi Zakawanu Garuba tare da direbanta ne a daren Litinin bayan an biya kudin fansa Naira miliyan 15.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar tare da direban nata ne a kan hanyarsu ta komawa gida Auchi, a Jihar Edo, kafin isowar gawarsa domin jana’iza.

Amma maharan sun ba su mahaifiyar marigayi Zakawanu wanda ya rasu a Abuja sakamakon rashin lafiya, ba su tafi da ita ba.

Rahotannin farko sun ce masu garkuwar sun fara bukatar kudin fansa Naira miliyan N20, bayan sun yi awon gaba da mutanen biyu a kan hanyar Abuja-Lokoja.

Wani dan uwan mamacin, Kadiri Garuba ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar ta Edo bisa yadda ta nuna musu tausayawa a lokacin jarabawar da ta same su.