✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara

Rarara ya wallafa bidiyonsa tare da mahaifiyarsa bayan ’yan bindiga sun sako ta

’Yan bindiga sun sako mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, da suka yi garkuwa da ita.

Mawakin da kansnne ya sanar da hakan tare da wallafa hotonsa tare da ita bayan an sako ta; kimanin kwana 20 ke nan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da dattijuwar a gidanta da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.

A cikin bidiyon, an ga Rarara zaune a kusa mahaifiyar tasa, yana rungume da ita

Ya kuma bayyana bayyana godiyarsa ga Allah da ya kungiyar da mahaifiyar tasa, tare da mika godiya ga mutane da suka taimaka da addu’o’i a kan lamarin.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa an wuce da mahaifiyar Rarara ne zuwa wani asibiti a Abuja domin duba lafiyarta.

Wani mazaunin garin Kahutu, ya bayyana cewa dattijuwar tana fama da hawan jini, kuma ya tsananta a lokacin da take tsare a  hannun masu garkuwa da ita.

A ranar 28 ga watan Yuni, 2024, ’yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, inda daga bisani suka bukaci kudin fansa Naira biliyan daya.

Daga baya sun rage kudin zuwa miliyan 900.

Yadda aka sace mahaifiyar Rarara

An yi garkuwa da Hajiya Halima  ne a ranar 28 ga watan Yuni, a gidanta da ke yankin Kahutu a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina.

Shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba  a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kadai suka dauka.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke dauke da su,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu.

Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin kauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan kauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,” in ji shi.