An sako dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu bayan ya shefe kwana tara a tsare yana fusknatar bincike.
An sakko shi ne daga Sashen Bincike Manyan Laifuka na Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya, inda aka yi ta tsare shi tun ranar Litinin 6 ga watan Yuli ne Jami’an tsaro na DSS suka kai shi gaban kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin binciken zarge-zargen da ake masa guda 12 kan jagorancinsa a EFCC.
“An saki Magu da misalin 6.00 na yamma har ya koma wurin iyalansa a Maitama”, inji lauyansa, Wahab Shittu.
Tun ranar Juma’a lauyan ya shigar da bukatar neman belin Magu wanda ake tuhuma da laifukna da suka hada da kasa bayar da bayani kan kudin ruwan da aka samu a kan kudan Naira biliyan 550 da aka kwato daga wasu barayin dukiyar gwamnati.
Binciken na kwamitin tsohon Mai Shari’a Ayo Salama, ya sa aka dakatar da tare da shi da daukacin darektoci da wasu manyan jami’an gudanarwan hukumar.
Sauran zarge-zargen sun shafi wasu gidaje a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, rashin ladabi da sakaci da aiki da kuma fifita wasu jami’an hukumar.