✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako Dan Majalisar Dokokin jihar Kaduna da aka yi garkuwa

An sako dan Majalisa dokokin jihar Kaduna Suleiman Ibrahim Dabo, wanda aka sace a jihar akan hanyar Zariya zuwa Kaduna. Aminiya ta samu labarin ‎cewa,…

An sako dan Majalisa dokokin jihar Kaduna Suleiman Ibrahim Dabo, wanda aka sace a jihar akan hanyar Zariya zuwa Kaduna.

Aminiya ta samu labarin ‎cewa, an sake shi ne da misalin karfe 8 na daren jiya. Babu wanda yasan ko an biya diyya kafin sakin nasa, rahotan na bayyana cewa, dan majalisar ya isa gida kuma yana tare da iyalansa a yanzu haka.

Majiyarmu a Zaria ta tabbatar da labarin sakin dan majalisar, inda wani mazaunin garin ya ce, “Eh, an sake shi da misalin bayan sallar Isha’i. Ba shi kadai aka saki ba domin akwai sauran mutane da ban sani ba,” inji shi.

Da wakilinmu ya tambaya ko an biya kudin fansa kafin a sako shi? Sai ya ce, “Ni ban san nawa aka biya diyya ba, amma dai an biya kudi,” in ji shi.

An dai yi garkuwa da dan majalisar ne a kusa da kauyan Farakwai a akan hanyar Kaduna zuwa Zariya.