Masu garkuwa da mutane sun sako dan kasuwar nan na Taraba Usman Mayo wanda aka sace kimanin wata guda da ya gabata a Taraba.
A makon jiyaAminiya ta ba da labarin dan kasuwar wanda ya bukaci danginsa da kada su sake ba da ko kwabo bayan masu garkuwa da mutanen sun ki sako shi alhali danginsa sun biya kudin fansa Naira miliyan 100.
Wakilin Aminiya ya jiyo cewa sai da aka sake biyan Naira miliyan biyar kafin aka sako dan kasuwar a ranar Talata.
Usman Mayo ya dawo gida, amma yana fama da rashin lafiya wanda hakan ya sa aka wuce da shi asibiti.
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Dabid Misal, ya ce ba su samu labarin sako dan kasuwar ba.