An kubutar da daliban jami’ar Ahmadu Bello(ABU) Zariya da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da yamma. Daliban da aka yi garkuwan da su ne: Fatima Jalingo, Maryam Bello da Umar Sagir, dukkan suna ajin karshe a jami’ar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sakin daliban.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna DSP Yakubu Sabo, ne ya tabbatar da hakan a jiya Laraba da Yamma, inda ya ce daliban jami’ar na cikin wadanda suka fada cikin tarkon masu garkuwa da mutanen ranar 26 ga Agusta 2019 a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“Dama suke nan wadanda ba a sako su ba a yanzu haka sun koma gaban iyayen su.” In ji DSP Yakubu.