Daliban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya (ABU) guda tara da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a karshen makon da ya gabata sun kubuta daga masu garkuwar.
Rahotanni sun nuna cewa daliban wadanda ke Sashen Koyon Faransanci na jami’ar na kan hanyarsu ne domin zuwa ‘Kauyen Faransanci’ dake Legas domin wani shiri lokacin da masu garkuwar suka yi musu kofar rago tare das ace su.
An dai sace su ne a tsakanin garuruwan Akilubu da Gidan Busa ta babbar hanyar sannan suka bude musu wuta tare da yin awon gaba da tara daga cikinsu.
A lokacin dai masu garkuwar sun sace mutum tara daga cikin 12 da suke cikin motar mai cin mutum 18 tare da neman a biya su Naira miliyan 270 a matsayin kudin fansar.
Mahaifiyar daya daga cikin daliban da aka sace mai suna Talatu Sani ta tabbatar da cewa masu garkuwar sun tuntubesu tare da neman su biya Naira miliyan 30 kafin a sako diyar tasu.
Talatu dai ita ce mahaifiyar wata daliba mai suna Elizabeth John Sani.
Daraktan Sashen Hulda da Jama’a na Jami’ar Auwalu Umar shima ya tabbatar da sako daliban amma ya ki ya yi wani karin bayani a kan hakan.
Auwalu ya ca an sako su ne da daren ranar Asabar kuma tuni suke koma ga iyalansu.