Dalibai 27 da malamai uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi sun kubuta.
Da yake sanar da hakan a ranar Alhamis, Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce daliban da malamnsu sun shafe kusan wata hudu a hannun masu garkuwa da su.
- Rikicin Filato: Fulani da Irigwe sun sasanta
- Abin da ya sa muka kai hari kasuwar Goronyo —Shehu Rekeb
“Annabawan Allah, wadanda su ne zababbun Allah, su ma Allah Ya jarrabe su; amma duk mutumin Allah Ya jarrabe shi ya yi hakuri tabbas ladarsa a wurin Allah ba ta da iyaka,” inji shi a yayin da yake bayyana sace daliban a matsayin jarabawa.
Ya ce wadanda aka sako din sun hada da dalibai mata biyu da maza 25, sai malamai maza biyu da mace daya.
Bagudu ya roki Allah Ya kubutar da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane, sannan “ana ci gaba da kokari domin ganin an kubutar da su.”
Gwamnan ya kuma ba da umarnin a duba lafiyar daliban da malaman nasu da aka sako sannan a ba su tallafin da suke bukata kafin a mika su ga iyalansu.