✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako 3 daga cikin daliban da aka sace a Kudancin Kaduna

Sanarwar ta ce uku daga cikin mutum bakwai din tuni suka dawo gida.

Kasa da awa 48 da sace wasu daliban makarantar St. Albertine Seminary a Kudancin Kaduna, an sako uku daga cikin su bakwai din da aka sace.

An dai sace daliban ne bayan wani hari da aka kai harin ranar Litinin.

Makarantar dai mallakar Cocin Katolika ce da ke kauyen Fayit, kan hanyar garin Kagoma da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.

Shugaban makarantun da ke karkashin Cocin Katolika na yankin Kafanchan, Rabaran Emmanuel Uchechukwu Okolo ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu ranar laraba da daddare.

Sanarwar ta ce uku daga cikin mutum bakwai din tuni suka dawo gida.

“Muna masu farin cikin bayyana dawowar mutane uku daga cikin daliban da aka sace, kuma muna godiya ga dukkanin wadanda suka taimaka mana da addu’a har zuwa sako daliban.

“Za mu ci gaba da yin addu’a don ganin an sako ragowar daliban da aka kwashe su tare,” Inji sanarwar.

Matsalar garkuwa da mutane da kuma satar dalibai domin neman kudin fansa dai na dada kamari a Jihar Kaduna da ma wasu Jihohin.