✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake zaban Najeriya a matsayin mamba a kungiyar ITU

An zake zabar Najeriya mamba a Cibiyar Kungiyar Sadarwa ta kasa da kasa wacce ake kira ITU. Zaben yana daga cikin shirye-shiryen babban taron da…

An zake zabar Najeriya mamba a Cibiyar Kungiyar Sadarwa ta kasa da kasa wacce ake kira ITU.

Zaben yana daga cikin shirye-shiryen babban taron da ke gudana a birnin Dubai na kasar Daular Larabawa. Mahalarta taron karo na 20 na cibiyar ITU ya sake zabar Sakatare Janar, Houlin Zhao wa’adi na shekaru biyu, kamar yadda sanarwar taron ta nuna jiya. Najeriya da sauran kasashen da aka zaba a cibiyar za su yi wa’adin shekaru hudu daga watan Janairu 2019.

Cibiyar ITU wacce ta shafe shekaru 153 a duniya kungiyar ce wacce ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya wacce aka kafa ta don tafiyar ayyyukan sadarwa a duniya baki daya.

Tun asali an kafa ta a shekarar 1865 a matsayin kungiyar kasa da kasa ta masu sadarwa inda hedikwatarta ke birnin Geneba da ke kasar Siwizaland. Najeriya ta zama memba na kungiyar ITU a ranar 4 ga watan Nuwamban shekarar 1961.

Baban taron ne ke tafiyar da Kungiyar ITU wadda ita ce kololuwar kungiyar wacce ta zabi manyan shugabanninta, membobi 48 na cibiyar da kuma membobin 12 na shugabanin gudanarwa kungiyar.

A hannun daya kuma Zhao wanda injiniyan sadarwa ne wanda ya yi aiki a matakai daban-daban a kungiyar ITU zai fara wa’adinsa na biyu da wa’adinsa na hudu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019.

‘Za mu ci gaba da sadar da wanda ba a sadar ba. Za mu karfafa alaka don aiwatar da burinmu na sadar da duniya ta yadda bayanai da kimiyyar sadarwa za ta zama wani abu mai kyau ga kowa da kowa’’ Inji sanarwar.