A karo na uku Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, ya sake tsawaita dokar kulle da karin mako guda a jihar.
A sanarwar da ya fitar a ranar juma’a Gwamnan yace matakin tsawaita dokar ya zama dole domin kare yaduwar annobar coronavirus a jihar.
Gwamnan yace matakin ya biyo bayan rashin biyayyar al’umar jihar ga dokokin gwamnati domin kare yaduwar cutar, ” Sakamakon haka, ya zama wajibi mu tsawaita dokar kulle har zuwa ranar 31 ga watam Mayu” in ji shi.
Yace matakin ya zama tilas domin kare yaduwar cutar, duk da yake ba abu ne mai dadi ba
Dokar kulle na cigaba da aiki a jihar Ogun tun bayan da gwamnatin jihar ta saukaka dokar a jihar, da jihar Legas da Yankin Babban Birnin Tarayya, domin a jihar Ogun gwamnan jihar ya daura daga inda gwamnatin tarayya ta tsaya, inda ya cigaba da tsawaita dokar har a karo na uku.