✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake sa dokar hana acaba a kananan hukumomin Legas 4

Yanzu yawan kananan hukumomin da aka hana zuwa 10

Gwamnatin jihar Legas ta sake kafa dokar hana haya da babura da aka fi sani da acaba a wasu kananan hukuminta guda hudu.

A ranar Alhamis gwamnatin ta kara wasu kananan hukumomi inda a yanzu yawansu wadanda aka hana zuwa guda 10.

Daukar wannan mataki na hana Acaba a kananan hukumomin a cewar gwamnatin shi ne don ta rage yawan aikata laifuka da kuma yawaitar hadura sakamakon tukin ganganci.

Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ya ce dokar za ta soma aiki ne daga ranar daya ga watan Satumba na shekarar 2022.