Gwamnatin jihar Legas ta sake kafa dokar hana haya da babura da aka fi sani da acaba a wasu kananan hukuminta guda hudu.
A ranar Alhamis gwamnatin ta kara wasu kananan hukumomi inda a yanzu yawansu wadanda aka hana zuwa guda 10.
- LABARAN AMINIYA: An Cafke Wani Da Bindigogi 8 A Tashar Mota A Abuja
- Ma’aikata sun yi barazanar rufe ilahirin makabartun Abuja
Daukar wannan mataki na hana Acaba a kananan hukumomin a cewar gwamnatin shi ne don ta rage yawan aikata laifuka da kuma yawaitar hadura sakamakon tukin ganganci.
Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ya ce dokar za ta soma aiki ne daga ranar daya ga watan Satumba na shekarar 2022.