✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kashe mutum 15 a kauyukan Katsina

A kalla mutum 15 aka kashe a daren ranar Laraba lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari a kauyuka hudu na Kananan…

A kalla mutum 15 aka kashe a daren ranar Laraba lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari a kauyuka hudu na Kananan Hukumomin Kankara da Danmusa duk a jihar Katsina.

Mazaunan garin sun fara kai harin ne a unguwar Unuwar Nagwande da misalign karfe 4:30 na yamma nan ta ke suka fara kashe mutum 4 kafin su shiga Unguwar Rabo su kashe mutum 9 sannan suka kai hari unguwar Gidan Daji anan suka halaka mutum 2.

Duk kauyukan na cikin Karamar Hukumar Kankara da ke jihar.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Maidabino a Karamar Hukumar Danmusa, inda suka shiga kasuwar garin dake ci suka budewa jama’a wuta.