A karshe gwamnatin Najeriya an kafara farashin zuwa fiye da Naira 165 a hukumance.
Duk da cewa a baya akan sayar da man a wasu gidajen mai akan sayar da man fiye da hakan, a ranar Talata ne aka kafa farashin hukumance.
Dillalan man fetur sun ce Gwamnatin Tarayya ta sahale musu karin farashin, kuma mun nemi jin ta bakin kakakin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur (NMDPA), Apollo Kimchi, a safiyar Talata, amma ya yi gum.
Jadawalin kafin farashin da ya fara aiki a ya nuna za a rika sayar da man fetur Naira N184 zuwa N189 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya — Karin na N24 shi ne mafi yawa.
A yankin Arewa ta tsakiya dkuma za a rika sayarwa N179, yankun Kudanci kuma N165 zuwa N179 ko da yake ana sayarwa N169 a Legas, a Abuja kuma N174.
An kuma kara farashin daga a gidajen mai da ke yankin Legas daga N148.17 zuwa daga N160 zuwa 162.
Manyan rumubuan mai a yankin Warri/Ogbarra sun kara farashinsu zuwa tsakanin N162 da N165 a Fatakwal kuma an kara zuwa tsakanin N165 zuwa N167.