✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kama daya daga cikin fursunonin kurkukun Kuje a Katsina

Fursunan ya shiga hannu yana tsaka da sayar da tabar wiwi.

Daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje ya shiga a hannu a Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

Tserarren fursunan Kamala Lawal mai shekaru 33, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda a garin Dan Musa a ranar Juma’ar nan.

Tawagar jami’an karkashin jagorancin DPO na Danmusa ce ta cafke Kamala bayan samun bayanan sirri.

Kakakin rundunar ’van sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya shaida wa manema labarai hakan, yana mai cewa tserarren fursunan ya shiga hannu yana tsaka ta sayar tabar wiwi.

Fursunan da aka kama

SP Gambo ya ce da zarrar an kammala bincike a kan Kamala, rundunar za ta mayar da shi hannu Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 5 ga watan Yuli ne wasu ’yan bindiga suka far wa gidan yarin na Kuje da ke babban birnin kasar, inda suka kubutar da mutane da dama, ciki har da fursunonin da ake zargin mayakan Boko Haram ne, wadanda ake tsare da su.

Tun bayan kai harin ne Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya (NCoS), ta fitar da sunaye da fuskokin ’yan ta’adda 69 daga cikin fursunonin da take nema ruwa a jallo.